Mai ciki ta mutu a Asibiti saboda rashin sabbin kuɗin da za ayi mata aiki a jihar Kaduna

Wata mai juna biyu ta rasa ranta a asibiti sakamakon rashin sababbin ƙuɗi da za’a mata magani

A wani labarin da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa, ta bayyana cewa “wata mata mai dauke da juna biyu a Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru a Kaduna ta rasa ranta sakamakon rashin sababbin ƙuɗi da za’a biya a asibiti domin yi mata magani.

Sanarwar da aka bayar ta bayyana cewa, James Auta, wanda shine mijin marigayiyar, ya ce “asibitin ya ki basu kulawar gaggawa a lokacin da ya kasa biyan kudin saboda karancin sababbin kuɗaɗe.

Ya ƙara da cewar “Na ruga zuwa bankina domin in ciro kudi amma aka ce babu. Na koma wajen masu POS, amma ban samu ko daya ba, domin tun da aka fara batun sabon kudin, galibin ma’aikatan POS sun kulle cibiyar kasuwancinsu.”

Ya ci gaba da magana, ya ce, “Da yake na kasa cire kudin, sai muka yanke shawarar komawa gida, tare da dogara ga Allah ya kaimu lafiya, amma abin takaici, lamarinsu ya yi tsami, wanda ya kai ga mutuwarta.”

Ya ce matarsa ​​ta fara nakuda da misalin karfe 11 na dare, kasan cewar bani da sababbin ƙuɗi, sai na kirawo wata ma’aikaciyar jinya da ke unguwarmu, amma yayin da matata ta samu nasarar haihuwa, sai jini ya ɓalle mata,yana fita ba kakkautawa, duk da. Yunkurin da ma’aikaciyar jinya ta yi na dakatar da zubar jinin ya ci tura, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.

By 82b6ae23bc014cf3bebb56003ce43e5b

From Opera News.

Views: 29

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *