Masu zanga-zanga sun lalata banki a jihar Ibadan

: Masu zanga-zanga sun lalata banki a jihar Ibadan:

Masu zanga-zanga sun lalata reshen wani banki dake kan titin Iwo a jihar Ibadan.

Wasu matasa da direbobin motocin bas da kuma ‘yan kasuwa ne suka fito kan tituna domin nuna adawa da karin farashin man fetur da kuma karancin sababbin kuɗaɗe.

Takardun kudin Naira da aka sake fasalin da suka hada da N200, N500 da N1,000, an fara amfani da su ne a ranar 15 ga Disamba, 2022, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da su a ranar 23 ga Nuwamba, 2022 a Abuja.

Tun da farko dai CBN din ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin karbar tsofaffin takardun kudi na Naira, amma daga baya ya kara wa’adin zuwa 10 ga watan Fabrairu.

Mista Emefiele ya ce an tsawaita wa’adin ne domin baiwa ‘yan Najeriya da suka samu Naira bisa ka’ida kuma suka makale, damar saka kudadensu domin yin musaya.

Gwamnan ya umurci bankunan da su loda mashin dinsu na Automated Teller Machines da sabbin takardun kudi na Naira domin tabbatar da ‘yan Najeriya sun samu damar yin amfani da su.

©punchnewspapars.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *