Wasu Matasa 2 sunyi mace mai cikin wata 8 fyaɗe a abuja
Matasan sun sace matar ne kuma sun yi mata fyade duk da tana da cikin wata takwas da ta ke dauke da shi.
Wata kotu da ke yankin Gwagwalada a Abuja, ta tsare wasu makiyaya biyu da suka amsa laifin yin garkuwa da wata mata tare da yi mata fyade a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Maris.
Mai gabatar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa a ranar 25 ga watan Fabrairu, wadanda ake zargi, sun yi garkuwa da wata mata mai cikin wata takwas a gidanta da ke Karamar Hukumar Abaji.
Ya bayyana wa alkali cewa wadanda ake zargin sun kuma yi wa matar fyade a cikin dajin, ba tare da la’akari da cewa tana dauke da tsohon ciki wata takwas (8).
https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-lalace-zina-a-fili/
Ya ce wani Abubakar Wakili a Karamar Hukumar Abaji ne, ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sandan yankin Gwagwalada a ranar 26 ga Fabrairu.
Mai gabatar da karar, ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 96, 262, 264, 387 na kundin laifuffuka.
https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-lalace-zina-a-fili/
Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya dage yanke hukuncin ne domin ganin halin da mai juna biyun za ta tsinci kanta a ciki.
Daga nan kuma sai na dawo dan yanke masu hukunci dai-dai da laifin da suka amsa sun aikata.
Views: 307
