Milliyan 150 kuɗin kujerun zama na ne—Naziru Sarkin Waƙa

Milliyan 150M Basu Wuce Kuɗin Kujerun Zama ba—Naziru Sarkin Waƙa Yayi Martani Ga Rarara.

Shahararren mawakin Sarauta Wato Nasiru Sarkin Waƙa, yayi zazzafan Martani ga Fitaccen mawaƙin siyasa Adamu Kahutu Rarara.

Kwanakin baya ne dai Ɗan takar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyar APC Bola Ahmad Tinubu da mawaƙin shi Rarara suka yima Naziru Sarkin Waƙa tayin zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan 150M da Motar miliyan 80 akan suna so ya koma Jam’iyyar su ta APC, amma yaƙi amincewa da tayin nasu.

A wani faifan Bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tik-Tok, ya faɗi cewar “Wannan tayin ba shine na farko ba, anyi yafi sau ɗaya ko sau biyu, wannan na ƙarshe ne na baku shi yadda yake, wannan kuɗi da kuke gani ba wasu kuɗine ba a gurin ɗan siyasa idan ya baka su.

Dalili da yasa idan ɗan siyasa ya bani kuɗi bana amsa shine: duk mutuncin da kake dashi a wajensa duka ya ƙare, sannan ba’a wajen sa kaɗai ba, har a wajen wani ma.
Babu wani ɗan siyasa da zai ce maka na kawo masa faifan sidi nace masa ga wannan, har Buhari ya gama mulkinsa babu wani Minista ko gwamna daya isa ya fito yace nace masa ga abin da ya kamata aima ƴan kasa ko mawaƙa, akwai waɗanda suke laɓewa da hakan da zaran aka basu kuɗin sai suje suyi harkan gabansu kaɗai. Ni bazan iya yin irin wannan abun ba, kuma ba wanda zai taɓa cewa nai masa.

Na Rantse da Allah a matakin da nake yanzu Miliyan ɗari biyu 200M ba kuɗi bane ba.

Mu cancanta muka duba, mun duba miye zai tai maki ƙasar mu, miye zai taimaki al’ummar mu, da kuma addinin mu wanna shine mukai kuma Allah shine shaida, kuma ɗan takarar dana ɗauka indan dan a ɓatan raine na rabu dashi, to bazan rabu dashi ba.

Saboda haka duk wanda ya ƙarɓi kuɗin Bola Tinubu to yaje yasa su a Bola.

Mu Allah mukasa gaba kuma shi zai taimake mu.

Source by Hilal Haruna

Captured at @sarkinwaƙa.tik-tok

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *