Ana zargin ministan harkokin jiragen saman Najeriya Sen. Hadi Sirika da yin wasu kalamai game da zaɓen 2023 waɗanda suka sosa zukatan al’umma kuma ke ci gaba da yamutsa hazo a fagen siyasar Najeriya.
Hadi Sirika dai ya bayyana cewar “Muna da kuɗin da zamu bawa talaka da kuma tsaba don muci zaɓe”
Tayin da a gafe guda jam’iyyar sa ta APC ke ci gaba da gudanar da yaƙin neman zaɓen ta sassan ƙasar nan
A jihar Katsina.
A ranar Laraba 7/12/2022, tawagar dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Radda, suka sauka karamar hukumar Baure, domin cigaba da gangamin yakin neman zabe na 2023.
Shugaban yakin neman zabe, Arch. Ahmed Dangiwa, ya shaida mahalarta gangamin taron cewa karamar hukumar Baure tana da tarihi a jam’iyyar APC wanda a karamar hukumar aka fara gangamin yakin neman zabe na 2019 , kuma yana adduar cewa Allah yasa yadda aka ci zabe a wanchan lokacin, wannan karin ma da yaradar Allah za a samu nasara. Ya shaida masu cewa Asiwaju Bola Tinubu ya ba Shugaba Muhammadu Buhari gudunmuwa don haka ya kamata a maida mashi alkhairi da ya yima dan shiyyar Daura.
Ya kara da cewa Jamiyyar APC ta kawo alherai wanda alumma suka amfana daban daban, yayi kira akan cewa kowa ya koma runfar shi ranar zabe domin samun nasarar Jamiyyar APC daga sama har kasa.
Shima shugaban jam’iyyar APC, Alh. Sani Aliyu Daura, ya shaida cewa sun zo ne domin suyi godiya akan irin gudunmuwa da ake basu tin lokacin kafuwar Jamiyyar APC, ya bada tabbacin cewa ayyukan alkhairi da Jamiyyar da shimfida zata linka shi idan Allah ya basu nasara. Daga karshe yayi godiya tare da yi masu fatan alkhairi.
Da yake maida martani, Dr. Dikko Radda, ya shaida cewa Allah ya sa ma garin Baure albarka domin duk gangamin yakin neman zaben jam’iyyar na APC tun shekarar 2015 a nan ake fara shi. Ya kara da cewa a 2015 karamar hukumar Baure ta zabi APC da kuri’u 31,000, a 2019 kuma an samu kuri’u 41,000, yana fata wannan karin zasu linka abun da sukayi 2019.
Ya tabbatar masu cewa wannan gwamnati mai zuwa zata rike amanar su babu cuta babu cutarwa, in Allah ya yarda talakan jihar Katsina zai san an kafa Gwamnati idan Allah ya bada nasara. Yayi kira ga matasa, mata da marayu, da cewa Allah ya kawo mai ceton su, matashi, mai kwazo, mai jini a jika. Ya bada tabbacin cewa zai taimaka ma mata na jihar Katsina domin su taimaki ma yayan su, al’ummar su.
Ya ja hankalin su da cewa, idan yan adawa suka zo zo wajen su, zasu zo da salan yaudara, zasu ce babu tsaro da maganar yunwa, yace masu an wuce lokacin yaudara kuma duk wanda zaya baka riga to ka kalli ta wuyan shi.
Ya kara da cewa, ya rike Karamar hukuma kuma kowa yasan irin kyakyawan shugabanci da ya kawo, sannan ya shaida cewa akwai wadanda suka rike dama irin ta amma basu taba abun azo a gani ba.
Daga karshe tawagar ta shiga mazabu goma sha biyu na karamar hukumar Baure domin ganawa da masu ruwa da tsaki domin neman alfarma da goyon bayan su.
Daga: #GwagwareMediaReporters
Views: 15
