
Rahotanni daga kasar India na cewa, wani mutum a arewa maso gabashin Indiya, wanda ya fi yawan iyali a duniya, ya mutu.
Ziona Chana mai shekaru 76. Iyalinsa sun ce ya yi fama da ciwon suga da hawan jini wanda yayi fama da su kafin mutuwarsa.
Mr, Chana yana da mata 39 da yara 94 wadanda ya haifa da kuma jikoki da yawa a raye
Mutumin ya zauna tare da dukkanin iyalinsa a wani gida bene hawa hudu da ke wani kauye mai tsaunuka a jihar Mizoram, da ke iyaka da Myanmar.
Hukumomi sun ce gidan ya zama wani babban wurin jan hankali ga ‘yan yawon bude ido saboda yawan iyalin da Allah ya hore wa mutumin.
Mr Chana ya shugabanci wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke ba da damar auren mata fiye da daya a duniya.
Mutumin ya fara yin aure yana da shekara sha bakwai da haihuwa
Views: 76
