NCC ta bayyana babban dalilin da ya sanya datar mutane ke saurin ƙare wa

  • Ƴan Najeriya na cigaba da yin korafi akan rashin sanin dalilin da yasa datar su ke saurin zuƙewa
  • Wasu masu amfani da Data sunce an ragewa datar nagarta ne
  • Yayin da wasu suke zargin kamfanonin da suke siyan data da “Sibaran-nabayyen” yar datar da suka siya

Abuja – Hukumar sadarwa ta Najeriya tace ta damu da korafe korafen da ƴan ƙasa ke cigaba da yi mata.

Korafin da ƴan Najeriya ke faman zabga mata shine akan yadda ake sukuwar sallah akan datar da suka saya ta sati, wata ko shekara.

Wannan dalili yasa hukumar sadarwar ta Najeriya, tayi fargar daji wajen gano ummul-aba-isin da yasa hakan ke faruwa.

Masu amfani da Data suna fuskantar zuƙewar data, kuma suna mana ƙorafi a NCC. “

Ya cigaba da cewa:

“Illar da aka samu ta COVID-19 itace babbar jigo a cikin matsalar, domin ta haifar da samuwar sababbin ababen kimiyya da fasaha.”

Ya ƙara da cewa:

“Hakan ne yasa aka samu sababbin hanyoyi nayin abubuwa a duniya.

“Harkar sadarwa a Najeriya itama abin ya taɓa ta, saboda an samu shigowar manya manyan na’ura masu ƙwaƙwalwa, agogo mai waya, da sauran kayan zamani masu kyau wanda yabawa masu amfani da waya damar zaɓi maras adadi”.

Ya shaida wa jaridar Thisday cewar:

“Hakan yasa aka shiga amfani da fasahar wajen amfani da kafafen sadarwa na zamani, da tura saƙo na ujula.”

“Ko shakka banayi, babban abinda yake sawa abubuwan nan suyi aikin su yadda yakamata shine mahaɗa (Network).”

Ya ƙarkare da:

“To nan batun zuƙewar data tazo, domin idan da mahaɗa mai kyau, za’a samu yin abu yadda ya kamata, daga nan kuma data zata zuƙe, shine mutane suke cewa ana cire musu data ba bisa ƙaida ba.”

source:hausa.legit.ng

Views: 37

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *