Sheakh Dahiru Bauchi ya maida martani kan kisan yan tijjaniya a Jos

Sheakh Dahiru Bauchi

KISAN ‘YAN TIJJANIYA A JOS

SAKON SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI Ga AL’UMMAR MUSULMI;

SHEHU Ya Ce;

“Mun Yi Imani Wadannan Bayin ALLAH Kwanakinsu Ne Ya ‘Kare, Don Haka Ko Da a Gida Suke Yau Zasu Tafi,

Amma Da Yake ALLAH Yana Sonsu Da Samun Shahada, Sai Ya Basu Iko Suka Yi Tattaki Tun Daga Jihar Ondo, Zuwa Bauchi, Donmin Taron Girmama Kalmar; LA’ILAHA ILLALLAHU….

Jiya Mun Yi Zikirin Juma’ah Tare Da Su Sun Yi Zubin Adashensu Na; LA’ILAHA ILLALLAHU… Mai Yawa, Kuma Yau Da Safe, Sun Yi Lazimin Safe Sun Yi Hailala, Sun Yi Salatin ANNABI, Sun Yi Istigfari,

Dama Hikimar Shiga Tijaniyya Kenan Ko Da Yaushe Kana Shirye Ga Mutuwa, Hakika Wadannan Mutane Sun Yi Babban Rabo Sun Fito Wurin Taron Girmama Kalmar Da Babu Kamarta a Duniya Da Lahira Suka Yi Shahada a Hanya, Kuma Dama Kowane Mutum Ya Kan Tafi Ne Akan Sana’arsa,

Daga ‘Karshe SHEHU(R.A) Yana ‘Kira Ga Al’umma Da Su Yi Hakuri a Kwantar Da Hankali, Ana Kan Bin Dukkan Hanyoyi a Hukumance Don Ganin An Bi Kadin Wadannan Jinane Masu Tsada Da Suka Kwarara”.

Muna Musu Fatan ALLAH Ya Karɓi Wannan Cinikayya Tasu(Tsakaninsu Da ALLAH(S.W.T), Ya Sada Su Da MANZON ALLAH(S.A.W), Ameeeeen.

Othman Muhammad
FITYANU MEDIA.

Views: 15

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *