Uba ya nemi surukansa su kwashe kayan sa ranar ‘yarsa da suka kawo saboda bidi’a ne

Ku kwashi kayan ku, mu baza mu wahalar da wanda zai auri ya’yan mu ba~Sheikh Abubakar Usman Mabera

A yau Assabar, wata tawagar jama’ar musulmi da suka fito daga Karamar hukumar mulki ta Wamakko, suka je neman auren wata mata a Hidikwatar kungiyar Izala Jos reshen jihar Sokoto, wajen shugaban majalisar Malamai na Jihar Sokoto, kuma babban limamin masallacin Mallam Buhari Dan Shehu dake nan cikin birnin Sokoto, wato Sheikh, Imam Abubakar Usman Mabera.

Abin ya faru shine: Lokacin da suka gabatar da abin da ke tafe dasu na nemawa ‘dan su mata, Imam Abubakar Usman Mabera ya basu kamar yadda shari’a ta tanada. Daga nan ne sai wadannan mutane suka fita waje, can sai suka sake dawowa cikin Office kowanensu dauke da Kwalayen minti, cingam, Biscuit, da Katon-Katon na lemu iri daban-daban da Goro, kamar dai yadda bakar al’adar da ake yi a jihar Sokoto tayin kayan SEE I LOVE, wadanda ake kusan kwashe dubu 300,000 ta tanada. Suna shigowa da su sai daya daga cikin su yace Allah ya gafartawa Mallam ga godiyar mu akan alherin da kukayi muna inji yaron da ya turo mu.

Sai shugaban Majalisar Malamai Ash-Sheikh Imam Abuakar Usman Mabera ya daga kai ya kalle su ya kalli tarin kayan da suka jibge, yace lallai ma kuwa!!….A nan Ofishin Izala za’a shigo muna da wannan abin Qyama?…. Yau Bid’ah ce har cikin gidan Izala?…Sai ya ce su kwashe kayan su su maida masa ya bude shago dasu ya samu abin biyan Sadaki.

Imam yace bamu da wani aiki sai bi gari wa gari muna yaqi da irin wannan Bidi’a yanzu ace mu za’a kawo ma wannan mu amsa?……Sam ba zata sa6u ba bindiga a ruwa….

Hakika ya kamata wannan kyakkyawar dabi’a ta shiga cikin zukatan kowane musulmi musamman shugabannin mu da Sarakunan mu wadanda su ne ya kamata su hana irin wannan mummunar bidi’ah.

Wadannan Mutane sun koma da Kayansu cike da mamaki cewa basu taba ganin irin haka ba sai a Yau.

Ubangiji Allah ya karawa Malam lafiya tare da kariya.

©Gaskiya Media Tv

Karin Labarai

DANGANE DA TSARIN SABON COVID 19 AKA BUDE RANAR JUMA’A ..

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu al’ummar musulmi ..

Da farko ina bamu shawara cewa duk wanda yazo cika wannan tsarin na covid 19 da ake cikewa yanzu idan yana bashi wahala ko kuma baisan yadda xai cika ba yayi tambaya, Idan kayi tambaya aka baka amsa kakasa ganewa tau karoka acika maka kokuma kabiya kudi acika maka…

Babban abinda yassa mutanen Arewa basu samun wasu tallafe-tallafen gwamnati da kuma bashi da gwambnati ke bayarwa babu kamar rashin bin ka’idar yadda za’a cike wannan tsarin da aka fitar…

Saboda haka dangane da wannan tsarin na Covid19 da ake cikewa akwai bangarori guda ukku kamar haka;

Covid19 house hold
Akwai covid19 sme
Akwai ageimeis ..

Dukkansu wadannn tsarin basukka ne na gwamnatin tarayyya amma bazaka taba cin gajiyarsu ba dole sai kabi ka’idar yadda za’a cike wannan tsarin ..

Covid19 household zaka samu kama daga miliyan daya zowa kasa , Wannan tsarin kowa da kowa zai iya cika shi swabanin covid 19 SME

Covid19 sme kuwa dole sai kanada takardar rijistar kasuwancinka wato CAC domin tabbatarwa gwamnati kai cikakken Dan kasuwa ne …

Haka zalika shima ageimeis sai kayi training tare da takardar shaidar kayi training din…

Dan haka ina bamu shawara matukar mutun yana da hali yacika tsarin SME covid19 saboda samun kudi masu yawa domin bunkasa harakar kasuwancinka saboda zaka samu naira miliyan biyu da rabi zuwa kasa ..

Don haka mai shawar cika wannan tsarin na Covid19 SME bayada CAC yayi magana insha Allahu zamu ara masa CAC akan kudi kalilan domin taimakon kanmu da kanmu

Allah yasa mudace dan Allah duk wuyar cika wannan tsarin na covid19 karka gaji kacika insha Allahu xa’a samu nasara a wannan Gwamnatin.

Sai dai irin wadanna tsare tsaren da gwamnati ke kawowa ana zargin yan kudu sunfi yan arewa cin gajiyarsa kamar yadda za kuga ra’ayin wani matashi ga abibda yake cewa.

YAN KUDU SUNFI YAN AREWA NATSUWA WAJAN CIKA PORTAL NA GOVERNMENT

Slm,Wanann yana daya daga cikin dalilin dayasa Mu yan arewa bamucika samun tallafi ko loan na government ba saka makon idan aka bude portal most of us ba ma tsayawa muyi going through akan portal din.

Kawai mutun daya bude portal sai ya tafi wajan cike form batare dayasan mai zai saka awajanba dan allah muringa tsayawa Muna karanta criteria for application.shiyasanya mu yan arewa kullin muke jajen muncike Abu Amman bama samu ba

dalili shine yan kudu sunfi mu natsuwa su karanta dokokin portal Wlh wani dan kudun sai yayi 24hours yana karanta criteria for application sai yagama fahimta complete sannan sai yaje yayi apply a nutse kuma dazarar anfara approved zakaga sune gaba gaba anayimasu alert!!!

mukuma munzama sakarkaru komai sai dai muringa sauri kokuma idan Abu yazo mukaryata wadannan duk halayyar mln bahaushene dan allah mugyara halinmu idan har munaso idan muncika abu muringa samu
Akwai abubuwa dayawa da munsan muncika Amman haryanzu shiru kamar ku danna wannan link don cikewa http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfhousehold

MSME CLINIC
8th matcht
Covid19 2021 application
Da dai sauransu,kuma tabbas nasan angama dasu, tau gaskiya sai mun gyara halinmu idan munaso muringa cin gajiyar abin gwamnati idan mutum bai San abuba yayi tambaya idan har munsani zamu baka amsa kuma kaima karinga karanta abu kafin kayi register, yanzu waye wa ta zo sosai ta yadda basaikaje wata CAFE ba dan zaka cika wani karamin abuba da wayar hannunka ma zaka iya cikawa

Allah yabamu sa’a baki daya daga COMRADE MUJAHEED

Views: 76

3 thoughts on “Uba ya nemi surukansa su kwashe kayan sa ranar ‘yarsa da suka kawo saboda bidi’a ne

  1. Assalamu’alaikum Malam Dan Allah Inada Tambayoyi Ukku Kamar Haka: Shin Malam Idan Ankarbi Bashin Wa’adin Sati,ko Wata Nawane Goverment Zata Bawa Mutane Kamin Fara Biyan Bashin?? Tambayata Ta Biyu Kuma Itace Ni Dan Jahar Nejane Taya Zanyi Nasamu CAC Number Agurinku??

  2. Tambayata Ta Ukku Itace Ta Karshe Shin Dan Allah Zan Iya Anfani Da Karamar Wayata Yar Kirar Vivo Domin Yin Register?

Leave a Reply to Umar Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *