VIDEO: “Kowa yaci gaba da gininsa babu wanda ya isa ya rushe har yanzu nine gwamnan Kano”—Ganduje

Ku kalli hoton Bidiyon jawabin Gansuje

Ka Jira A Rantsar Da Kai Tukunna, Har Yanzu Ni Ne Gwamnan Kano, Don Haka Kowa Ya Cigaba Da Ginin Sa, Martanin Ganduje Ga Abba Gida-Gida

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf da ya yi hakuri tare da daina fitar da sanarwa a hukumance ta hanyar ba da shawara ga jama’a domin kada a haifar da rudani da bai kamata ba a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Juma’a a matsayin martani ga umurnin da ofishin zababben gwamnan ya fitar, inda ya gargadi mutane, kungiyoyi da suke gudanar da gine-gine a wuraren taruwar jama’a da su kiyaye.

A jawabin Gwamnan ya ce matakin da zababben gwamnan ya dauka ya saɓa da manufofin gwamnati domin har yanzu Gwamna mai ci bai cika wa’adinsa ba.

A cewar Ganduje, dangane da batun rabon mukamai kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da zama gwamna mai ikon zartarwa har zuwa ranar 29 ga watan Mayu kuma yana da hakkin gudanar da ayyukansa a na maslahar jama’a ko a jajibirin saukar sa.

“Har sai Abba ya zama gwamna a ranar 29 ga Mayu, ne yake da iko, amma zuwa Yanzu zai ci gaba da zama zababben gwamna kuma ba shi da iko na Gwamna.

Sanarwar ta kara da cewa, babu wani zababben gwamnan da yake da ikon a tsarin mulki ko doka na tantance alkiblar jihar har sai an rantsar da shi.

Ganduje ya bayyana cewa gwamnonin jihohi suna da iko, wajen rabon filayen don haka kowace gwamnati ta yi irin wannan aiki ciki har da gwamnatin da ta shude wacce zababben gwamnan yake yiwa biyayya ~ Cewar Gwamna Ganduje

Views: 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *