Video: Ku kalli yadda aka maida kabarin mahaifin Kwankwaso wajen yaƙin neman zaɓe

A yammacin ranar talata ne shafukan sada zumunta a Nijeriya suka cika da hotunan mai girma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da na mai girma tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Inda gwamna Ganduje ya ziyarce sa domin yi masa ta’aziyyar rasuwar ɗan uwansa daga bisani kuma ya ziyarci kabarin mahaifin Kwankwason.

To sai dai wani abun ban mamaki shine yadda dukkannin ɓangarorin biyu suka mayar da wajen tamkar wajen yaƙin neman zaɓe yadda aka ga magoya bayansu na yiwa ko wane ɓangare addu’a da fatan samun nasara a zaɓe.

Ku danna wannan link don ganin abinda ya faru.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=3020874221519110&id=100007896842960

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *