Video: “Kwankwaso ya bayyana matakin da zasu ɗauka idan aka tafi Inconclusive a zaɓen 2023”

Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.

Eng Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya zama wajibi a wannan karo hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tashi tsaye ta ƙara tsaftace harakokin zaɓe a ƙasar nan.

Tun daga matakan ƙananan hukumomi jihohi dama tarayya don tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe mai tsafta a kakar zaɓen 2023 dake tafe.

Kwankwaso ya ƙara da cewa yin hakanne kaɗai sahihiyar hanya ta tabbatar da Dimokuraɗiyyar gaskiya da adalci da kawo zaman lafiya.

Game da Inconclusive, Kwankwaso ya ce a wannan karon ya kamata shugabannin zaɓe su gyare kura kuren da suka tafka a baya domin kuwa wannan karon jama’a ba zasu lamunci irin wannan zaɓen na Inconclusive ba.

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *