Yadda Gwamnan jihar Gombe ya gina katafariyar kwalejin karatun Allo

Gwamnatin jihar Gombe ta gina katafariyar kwalejin karatun Allo a jihar domin saita karatun Almajiranta yayi dai dai da na zamani.

Ƙarin hotunan wasu daga cikin sassan katafariyar kwalejin karatun Alkur’ani mai girma da Gwamnatin jihar ta Gombe ta gina.

JINJINA GA GWAMNAN JIHAR GOMBE:

ra’ayin wani mai amfani da shafin Facebook.

Haƙiƙanin gaskiya Gwamnatin Jihar Gombe tayi abin faranta zukatan mu wajen gina katafariyar Tsangaya ga ma’abota karatun Allo.

An inganta ginin Tsangayar tare da samarda ɗakunan Kwana ɗauke da Gadaje, banɗakuna da ɗakin girki tareda wuraren da Almajirai zasuci abinci da wurin wankin kayansu.

Babu shakka wannan aikin na Gwamna Inuwa shi yakamata ace Gwamnonin Arewa sun ɗauka su faɗaɗa shi a dukkan ƙananan hukumomin su kamar yadda ake samarda makarantun Boko.

Da aiki ake yin gyara bada kafirin surutu ba.

Allah yataimaka wa duk Gwamnatin data damu da damuwar al’umma.

Views: 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *