
Wani mutun ne yazo inda ake aunar Masara a kasuwa Yana zuwa shima ya Buda buhu yace a bashi kwano biyar aka zuba masa ana karkarbar kudi akazo kansa Yace yabayar akace bai bada kudi ba Yace ya bayar can sai wani mutun a gife ya kirashi yace masa Mallan Dan Allah Ka bada kudin yace masa Wallahi Ban bayar ba wallahi yace to akara masa kwano biyar Goma kenan nan take wani yace aje a bashi Shinkafa kwano biyar aka Kai Masara aka nuko aka Dorawa Mashin akace a kaishi Gida Yana zuwa Gida Yayan sa Suna fitowa suna karbar garin nan Suka dinga Hambuda a Baki Wallahi.
Yace Wallahi rabansu da Dora abinci a gidan sa Kwana Takwas makaranta ma Wallahi bazasu iya zuwa ba.
Ya Allah Karabamu da Talauci Ya Allah Muna Rokon Ka kada Ka Jarrabe mu da Yunwa, Ya Allah Ka Azurta Kowa da Abinda Zasuci da Iyalan Su.
© Zinariya
Views: 22

Ingaski