Wurare 6 da ƴammata zasu samu Irin Mazan Aure da suka daɗe suna Mafarki
👉👉Wurin bukukuwan daurin Aure
Idan kina son samun miji cikin sauki dole ki kasance kina halartar wuraren taruwar jama’a musamman wurin daurin aure.
Wuraren daurin aure na samun halartar mutane daban-daban da mafi yawanci ba su da aure.
Amfanin neman saurayi a wurin daurin aure shi ne samun shi ba zai yi wahala ba saboda dole za a samu wanda ko wadanda suka san shi a wurin.
Shawara ga ‘yan mata, duk lokacin da aka gayyace ki bikin aure, ki yi gaggawar zuwa saboda baki san me zai faru gobe ba.
👉👉Taron karawa juna sani ko horo
Irin wadannan tarurruka na da muhimmanci wurin samun mijin aure mai irin tunanin budurwa, a nan ne za ki samu miji sai tunanin ci gaba da kuma hangen nesa.
Saboda yanayin taron da kika halarta, kina iya samun irin kalan mijin da ki ka dade kina hankoro a rayuwarki.
Kara karanta wannan
An Sha Shagalin Bikin Wasu Masoya Da Lemun Kwalba 2 Da Karamin Kek, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
👉👉Wuraren tarurrukan addini
Idan mace ta kasance mai son addini, irin wadannan tarurruka su ne wuraren da suka fi dacewa da samun miji na gari kuma mai tsoron Allah, cewar Premium Times.
Babbar alama ta samun miji na gari shi ne ya kasance ya na son addininsa da kuma halartar wuraren addini.
👉👉Wuraren motsa jiki
A irin wadannan wurare, mata da yawa sun samu mazajen da suke mafarkin kasancewa da su.
Mazaje da dama na halartar wuraren motsa jiki don inganta lafiyarsu da kuma samun nitsuwa.
Wannan wuri ne da za ki yi amfani da shi wurin fara wata mu’amala ta soyayya da wani wanda ya kwanta miki a rai.
Akwai hanyoyi da dama da za ki fara magana da wani a wurin, misali ki nemi taimako a wurin shi na koya miki yadda ake amfani da wani injin motsa jiki a wurin, daga nan komai na iya faruwa.
Kara karanta wannan
Yajin Aiki: Mace Mai Ciki Da Jaririnta Sun Rasa Rayukansu Saboda Rashin Likitoci a Nasarawa
Wasu matan na son maza wadanda ke gina jikinsu ta hanyar motsa jiki, idan kina daya daga cikinsu, kakarki ta yanke saka.
👉👉Taron kungiyoyin ayyukan sa kai
Mafi yawan mutane yanzu ba su fiye yin ayyukan sa kai da taimakon jama’a ba, ba tare da samun ko kwabo ba, cewar My Dating Hacks.
Alamun miji na gari shi ne wanda ya sadaukar da kansa don ya taimaki mutane ba tare da an biya shi wasu kudade ba.
Saboda haka, shiga irin wadannan ayyuka zai taimaka miki wurin samun mijin da ya dace da ke.
👉👉Wuraren wasanni da bukukuwa
Mafi yawan maza na sha’awar harkokin wasanni da suka hada da kwallon kafa da kwallon kwando da sauransu.
Yayin da mata kuma a bangaren su ba su cika damuwa da wasanni ba.
Zuwanki irin wadannan wurare zai jawo hankalin mazaje zuwa gare ki saboda babu ‘yan mata a wurin sosai, daga nan komai na iya kasancewa.
Views: 28
