Gwamna Zulum Ya Ziyarci Bankunan jihar a Borno
Daga Abubakar Saleh
Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci manya manyan bankuna dake birnin Maiduguri domin ganewa idanunsa wahalar da talakwan jiharsa ke sha wajen cire kuɗi a ATM.
Gwamnan ya ziyarci bankunan jihar Borno da suka hada da; Tag Bank, Zenith, UBA, Access, da sauransu.
A yayin ziyarar, yi wa talakawa alƙawarin da su kwantar da hankalinsu nan bada jimawa ba gwamnatinsa za ta kawo wasu tsare-tsaren da talakawa za su samu kuɗi cikin sauƙi ba tare da wahala ba a jihar.
©Zuma Times Hausa
Views: 45
