Yadda wani Ɓarawo ya tsere da Motar Miliyan 55 daga ɗani a wajen siyar da Motoci
Mohammed Manga ya bada labarin yadda su kayi da wani mai sayen mota da ya yi masu katuwar sata.
Shugaban kamfanin motocin Daggash Auto ya ce a wajen duba ingancin mota, aka dauke GLB 250
Farashin motar a kamfanin Mercedes Benz ya kai N55m, an sanar da ‘yan sanda abin da ya faru
Abuja – Mohammed Manga ya samu kan shi a halin ha’ula’i bayan da wani da ake tunanin abokin ciniki ne ya tsere masa mota ta miliyoyin kudi.
Mohammed Manga ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya ce wani da aka sani da suna Henry, ya sace masu motar Marcedes Benz kirar GLB 250.
Wannan lamari ya faru a garin Abuja yayin da wani abokin kasuwancinsa ya zo da Henry wurin saida motocinsu da nufin yi masa ciniki mai tsoka.
Benz GLB 250
Motar Benz GLB 250
Bayan an kai mota ga wannan Bawan Allah da aka ce sunansa Henry, sai aka yi ciniki, aka amince a kan farashin da za a saida abin hawan.
Rahoton PUNCH Metro ya ce daga nan sai mai niyyar sayen motar ya bukaci a ba shi damar ya zagaya da ita domin jin lafiyar abin da zan saya.
Za a sha man fetur
A cewar Mohammed Manga, abokinsa ya shiga marsandin tare da Henry domin yin gwaji, daga nan sai ya nemi ya cire kudi saboda a kara fetur.
A lokacin da wannan mutumi ya fita daga motar domin zuwa shagon POS a unguwar Garki, kwatsam sai mai karyar niyyar sayen mota ya tsere.
Kamar yadda Manga yake fada, babu cunkoso a kan titunan Abuja, a haka aka sace marsandin da ake saida a kan fiye da Naira miliyan 50 a yau.
An sanar da hukuma da jama’a
Tuni ‘dan kasuwan ya sanar da sashen hana sace-sacen motoci na rundunar ‘yan sanda, ya fada masu launin motar da adadin tafiyar da ta sha.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na reshen Abuja, Josephine Ameh ta ce jami’an tsaro su na bibiyar motar da nufin a cafke wanda ake zargin.
Shugaban kamfanin motocin na Daggash Auto ya nemi taimakon al’umma a shafin Twitter, ya roki su sanar ta lambar waya domin samun la’ada.
Views: 16
