Yadda wani Miji ya Auro Mata 3 a rana ɗaya domin huce takaicin Matar sa da tayi Yaji

Yadda wani Miji ya Auro Mata 3 a rana ɗaya domin huce takaicin Matar sa ta farko da tayi yaji

Wani mutumin Shanwe da ke yankin Katavi a Tanzania ya girgiza mutane saboda abin da ya aikata.

Athuman Yengayenga ya auri mata uku a rana daya saboda huce takaicin guduwa da matarsa ta yi ta bar shi


Ya ce ya so ya auri mata hudu saboda ko da wata ta gudu zai tsira da sauran ba tare da shiga matsala ba

Wani mutum ya kashe jama’a da mamaki inda ya auri mata uku a rana daya a wani gagarumin biki.

Athuman Yengayenga ya shiga masallaci da zankada-zankadan ‘yan mata da nufin aurensu gaba daya, Legit.ng ta tattaro.

Bayan Matarsa Ta Tsere: Wani Ya Auro Mata Uku A Rana Daya Don Huce Takaici, An Yi Gagarumin Biki
Mutumin Tare Da Mata Ukun Da Ya Auro A Rana Daya A Wurin Biki. Hoto: AZAM TV. Asali: UGC

Yengayenga wanda mazaunin Shanwe ne da ke yankin Katavi a Tanzania, ya ce ya yi niyyar auren mata hudu saboda bacin rai.

Ya ce ya auro mata uku a rana daya ne don huce takaici
Ya ce matarsa da suke tare ta gudu ta barshi shiyasa ya auri mata hudu don huce haushi, cewar AZAM TV.

A cikin hikimarsa shi ne idan ya auri mata da yawa, ko da daya ta gudu zai tsira da sauran.

Matan nasa Fatuma Rafaeli da Asha Pius da Mariam John sun bayyana yadda suke ji da auren namiji daya.

Sun tabbatar cewa dole a samu kishi tun da dukkansu ‘yan Adam ne, amma za su yi kokari don samun zaman lafiya a tsakaninsu.

Matan sun bayyana yadda suke ji da auren
Cewar uwargida Fatuma, yayin da ta ke gyara hijabinta:

“Har yanzu ba mu cika ba, muna bukatar mace guda daya.”
Mafi yawan ‘yan uwan Yengayenga suna auren mata da yawa, hakan ba wani abin mamaki ba ne a al’adarsu.

Amma auren mata uku a rana daya ya yi matukar ba wa ‘yan uwan nasa mamaki saboda ba su saba gani ba.

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *