Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya haramta sana’ar jari-bola a faɗin jihar baki ɗaya
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya haramta sana’ar jari-bola a faɗin jihar baki ɗaya
Ya bayyana hakan ne bayan cin karo da tarin kayan gwamnati da ya yi a wani waje na sana’ar jari-bola.
Gwamnan ya ce sun ɗauki matakin ne don kare masu sana’ar daga hare-haren ‘yan Boko Haram
Maiduguri, Borno – Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da haramta sana’ar jari-bola a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 27.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi ranar Litinin, a Maiduguri babban birnin jihar Borno, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dalilin Gwamna Zulum na hana sana’ar jari-bola
Zulum ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki wannan mataki ne domin kare masu sana’ar daga kisan da ‘yan ta’addan Boko Haram ke yi musu a wurare daban-daban na jihar.
Haka nan kuma Zulum ya ce an ɗauki matakin domin daƙile sace-sacen wasu kayayyaki na gwamnati da ake tunanin wasu daga cikin masu sana’ar ta jari-bola na yi.
A kalamansa:
“A cikin shekaru biyar da suka gabata, an kashe mutane da dama sakamakon harkar bola-bola.
Hakan ya sa gwamnatin jihar Borno gudanar da bincike dangane da sana’ar.”
“Kun ga wannan wurin, duk kadarorin gwamnati ne kuma a bayanku akwai kadarorin kamfanonin sadarwa.”
“Irin waɗannan ayyukan sai dai a kirasu da zagon ƙasa ga tattalin arziƙin Gwamnatin Tarayya da na jihohi.”
“Don haka na ba da umarnin hana jari-bola a dukkanin ƙananan hukumomi 27 har zuwa abinda ya sawwaƙa.”
Gwamnatin jihar Borno ta yi asarar kadarorin na biliyoyin naira saboda ‘yan jari-bola.
Gwamnan ya ƙara da cewa an san ‘yan jari-bola da ɓata kadarorin gwamnati da na sauran al’umma a yankunan da rikicin Boko Haram yai ƙamari.
Ya bayyana cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin jihar ta yi asara ta biliyoyin naira daga ayyukan masu sana’ar ta jari-bola kamar yadda aka wallafa a shafin Tuwita na NTA.
Zulum ya ƙara da cewa dokar ta shafi har masu sana’ar siyan manyan ƙarahuna, da masu sassara ƙarahuna gami da jigilarsu a faɗin jihar.
Views: 15
