Yadda Wata mata ta ƙona wata ‘yar sanda da ‘ya’yanta guda biyu a Jihar Anambra

Wata mata ta kona wata ‘yar sanda da ‘ya’yanta guda biyu.

Jaridar Lifestyle a Najeriya ta tattaro cewa an kama wata mata mai matsakaicin shekaru bisa zargin kona wata ‘yar sanda da ‘ya’yanta biyu a Nnokwa, karamar hukumar Idemili ta Kudu (LGA) ta jihar Anambra.

Wandda ake zargin mai suna Nneamaka Nwosu, ‘yar asalin garin Amawbia a karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar, an ce ta yi mu’amala da marigayiyar ne a lokacin da ta koma gida bayan rabuwar aure.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce wandda ake zargin (Nwosu) ta je wurin ‘yar sandan ne jim kadan bayan ta zama ba ta da matsuguni, kuma tana matukar bukatar masauki sakamakon rabuwar da ta yi da mijinta.

“Da mijin ya sake ta, sai ta gaya wa ‘yar sandan da ta ba ta masauki a gidanta.

“A wannan rana mai muni, ta yi rigima da ’yar sandan da ta kai ga fada. Ta bugi ‘yar sandan a kai ta fadi ta sume.

“Da sauri ta daure ‘yar sandan da ‘ya’yanta guda biyu tare da igiya a cikin dakinsu sannan ta banka musu wuta tare da ginin,” in ji shi.

An tattaro cewa wani dan banga na yankin da kuma wasu mutanen kauyen da gobarar ta ja hankalin ta ne suka kama wadda ake zargin, a lokacin da take kokarin tserewa.

Views: 28

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *