Yadda CCTV Camera ta dauki hoton yaron gida na lalata da matar gida

Rahotanni daga Nairobi babban birnin kasar Kenya na cewa, wani magidanci mai suna Okkufou Issoula ya maka yaron gidansa gaban wata kotu saboda samunsa da kaifin yin lalata da matarsa.

Magidancin dai ya gabatarwa da lauyoyinsa wani fai fan bidiyo wanda a cewarsa na’urar daukar hoto ta CCTV da ya makala a gidansa ce ta dauke su lokacin da suke aikata lalatar, wanda kuma a cewarsa dukkansu basubsan cewa ya makalata a gidan ba hatta mai dakin nasa bata san da Kyamarar ba.

Yayin da lauyoyinsa suka kunna bidiyon a bainar jama’a a cikin kotun yadda kowa zai gani kuma ya shaida, sai dai alkalin kotun ya ce bai gamsu da sahihancin fai fan bidiyon ba inda ya ce a je a gudanar da kwakkwaran bincike game da wannan lamari.

Kasancewar wanda ake tuhuma mai zaman yaron gidan mutumin ne mai shigar da kara da kuma matarsa, kuma dukkansu sun musanta aikata laifin.

Views: 22

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *