An sace amarya a Katsina gabanin daurin aurenta

Rahoton sashin Hausa na BBC ya bayyana cewa.

Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.

An sace Asama’u Dalhatu ana tsaka da shirye-shiryen soma bikinta, a cewar ɗan majalisar.

Ƴan bindigar sun kai hari ne kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskarin Katsina tare da sace Amaryar.

A lokacin tabbatar da faruwar lamarin, ɗan majalisar ya shaida wa jaridar Daily Trust cew an sace kanwar tasa da sanyin safiyar Lahadin.

Ya kara da cewa har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntube su ba domin neman kudin fansa.

Views: 65

2 thoughts on “An sace amarya a Katsina gabanin daurin aurenta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *