Yau za ayi gagarumin ruwan sama da ba’a taba yi ba a tarihin Najeriya

ALLAH YA MANA KARIYA:

Za a yi ruwan sama da iska da tsawa wadanda ba a taba yin irin ba a Arewacin Najeriya

Hasashen yanayi ya nuna matsalar da ba a saba gani ba ta ruwan sama da iska na iya faɗaɗa yayin da yanayin ke tunkarar yammacin Afirka da zai haifar da wasu munanan sakamako.

Hasashen ya nuna za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a wasu ƙasashen na yammacin Afirka.

Hasashen ya nuna za a maka ruwan saman ne a yankin Chadi da arewacin Najeriya da Burkina Faso da kuma wasu yankuna na Mali.

Za a maka ruwan sama mai tafe da iska da tsawa a arewacin Najeriya a gobe Talata, kamar yadda hasashen yanayin ya nuna.

Matsalar za ta kuma zafi yankunan Senegal da Mauritania zuwa ƙarshen mako.

Hasashen ya ce ruwan saman zai haifar da mummunan yanayi na ambaliya a yankunan na yammacin Afirka.

Ya Allah ka kare al’ummar musulmi daga duk wani bala’in su alfarmar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W

Sokoto Online

Views: 45

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *