LABARI DA DUMI DUMI: “Sojojin Najeriya sun kone kashi 40 na dajin Zamfara”

Rahotannin da ke shigo mana da dumi duminsu yanzu na cewa sojojin Najeriya, na can suna ci gaba da luguden wuta ta sama da ta kasa a kan sansanin yan bindiga masu tada kayar baya.

Hare haren na zuwa ne bayan shafe daren jiya suka kai musu hare hare ta sama da ta kasa a cikin dajukan da suka boye, yanzu haka dai rahotanni na cewa jami’an tsaron sun kusan kune kashi 40 na illahirin dajin.

Ko a jiya ma sashin hausa na BBC ya bada rahoton cewa,

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar ta ce sansanonin da aka tarwatsa a hare-haren sojin saman Najeriya sun haɗa da wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ake kira Dan ƙarami a ƙaramar hukumar shinkafi

A cewar sanarwar a baya ɗan fashin dajin ya fitar da wani bidiyo yana murna bayan artabun da suka yi da sojoji.

Views: 155