Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa auren dole ya sa mata ta kashe mijinta

Matashiya Rumasa’u; An yi mata auren dole ta kashe mijin har lahira

Daga Dattiasslafiy

Sunanta Rumasa’u Muhammad tana da zama a garin Wuro Yanka karamar hukumar Shelleng jihar Adamawa, shekarunta 19.

An daura mata auren dole da wani mutumi wanda bata so mai suna Muhammad Adamu dan shekara 35, ta nemi mijin ya saketa amma yaki, tabi duk hanyar da ya kamata ya saketa amma yaki, shine sai tayi amfani da wuka yana bacci ta burma masa a cikinsa.

Kafin a garzaya dashi Asibiti ya mutu, ‘yan sandan Shelleng sun kama matar, binciken farko na ‘yan sanda ya tabbatar da cewa an mata auren dole ne a ranar 6-8-2021, sati uku da yin auren ta kashe mijin.

Maigirma Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa CP Aliyu Adamu Alhaji ya bada umarni a gudanar da cikakken bincike a gurfanar da ita a kotu don ta fuskanci hukunci, sannan ya bada shawara wa al’umma su guji yin auren dole.

Ni kam a fahimtata babu dakikin mutum namiji kamar wanda ya nace akan sai ya auri matar da bata son shi, wannan wauta ne, kuma karshen abinda yake faruwa kenan ta kashe ka.

Yawanci iyayen yarinya idan makwadaita ne suna bada gudunmawa sosai wajen yiwa yaransu mata auren dole ga masu arziki.

Maza ku guji auren dole, babu dadi sam ka auri wacce bata sonka, ga mata nan birjik a gari sai wanda ka zaba, me zai kai ka ga auren dole imba wauta ba?

Allah Ya sauwake Ameen.

Views: 32

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *