Jerin kananan hukumomi 19 da aka haramta cajin waya a jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta dakatar da cajin waya a kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina

Cikin kananan hukumomin da abin ya shafa har da Funtua da Bakori da Malumfashi da.

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da hana sanar cajin waya a kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaro a duk fadin jihar Katsina.

An kuma kara wasu kananan hukumomin da suka hada da Funtua da Bakori da Malumfashi a cikin kananan hukumomin da dokar ta shafa.

Sune kamar haka.

Malumfashi

Funtua

Bakori

Jibia

Batsari

Safana

Dutsenma

Kankara

Matazu

Musawa

Kurfi

Faskari

Sabuwa

Dandume

Danja

Kafur

charanci

Kankia

Rimi

Za a iya tuna cewa Katsina Daily Post News ta rawaito maku cewa, dama can kananan hukumomi irinsu Jibia, Batsari, Safana, da Dutsinma, da kuma Danmusa da Matazu da Musawa da Kurfi na cikin kananan hukumomin dake fama da matsalar tsaron.

Sauran kananan hukumomin da wannan doka ta haramta cajin wayar ta shafa sun hada da; Kankara, da Faskari da Sabuwa da Dandume da kuma Danja.

Kwamitin tsaro na jihar Katsina wanda kwamishinan yan sandan jihar Katsina CP Sanusi Buba ke jagoranta, ya bayyana cewa, yan fashin daji da satar mutane na amfani da wuraren cajin wayar domin kai caji, tare da amfani da wayoyin nasu domin kira a kawo masu kudin fansa.

Views: 27

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *