Ko sauro ba zamu bari a raye cikin dajin Zamfara ba nan da zuwa faduwar rana—Rundunar Soji

Shugaban rundunar sojin kasan Najeriya Gen. Yahaya Faruq ya bayyana irin nasarororin da jakarunsa ke samu a yakin da suke gwabzawa tsakanin su da yan bindigar Zamfara.

Inda ya ce suna ci gaba da samun nasara, kuma ba sa son ki sauronsu rage a cikin dajin.

A wani rahoton kuma.

‘Yan fashin dajin sun kashe dan sanda 1, sun iza keyar mutum 23 a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun yi ajalin wani sifetan ‘yan sanda sannan sun yi garkuwa da mutane 23 sakamakon wani hari da suka kai Unguwan Maje da Unguwan Laka da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

TheCable ta fahimci yadda ‘yan bindigan suka kai farmakin da safiyar ranar Laraba.

An samu bayanai a kan yadda suka yi ta harbe-harbe ‘yan kauyen suna gudun neman tsira, TheCable ta ruwaito.

Wani ganau ya ce:
“Da farko sun fara kai farmaki Unguwan Maje ne, inda suka yi garkuwa da mutane 15 wanda yawancin su mata ne da yara.

“Daga baya suka nufi Unguwan Laka inda suka hallaka wani sifetan ‘yan sanda, Joshua Markus daga zuwan sa ziyarar ‘yan uwansa tun daga jihar Rivers.

“Yan bindigan sun yi garkuwa da mutane 7 ciki har da mata da diyar wanda suka hallaka.”

Wani soja mai murabus, wanda dan Unguwan Laka ne ya samu nasarar tserewa da iyalin sa dakyar. Sai dai sun babbaka motarsa da babur dinsa.

An ajiye gawar sifetan a asibitin Saint Gerald Catholic da ke cikin Kaduna.

Da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Mohammed Jalige, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.

Amma ya yi alkawarin bincike a kai, kawo lokacin rubuta rahotan nan , ba a samu jin komai daga bakinsa ba.

Views: 31

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *