Bidiyo: “Bana iya bacci ko tafiya saboda harsashin dake yawo a cikin cikina”—Zeenat Zakzaky

Bana Iya bacci ko tafiya, saboda harsashin da ke yawo a cikina – Matar Sheikh Zakzaky.

Uwargidan jagoran Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) wato Zeenah El-Zakzaky ta koka da irin radadin da take ji na halin da ta shiga sakamakon harsasan da ke yawo a cikin ta na harbi da Sojojin tsohuwar Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari suka yi mata a Zariya.”

An harbe ta ne tare da mijinta, Sheik Ibraheem El-Zakzaky a Zariya, jihar Kaduna a ranar 14 ga Disambar shekerar 2015, inda Sojojin suka kwashe tsawon kwanaki biyu suna luguden wuta kan daruruwan mabiya Shi’a.

https://apahausa.com.ng/video-kai-jamaa-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-koma-tamkar-indiyawa/

Sama da gawarwakin mutane 300 ne sojoji suka binne a asirce a wani kabari, a cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch.

A halin yanzu Zeenah ta ce tana fama da mugun ciwon ciki wanda ya hana ta komai.

Ta bayyana hakan ne a ranar Asabar din da ta gabata a yayin taron ranar Qudus a birnin Abuja.”

Views: 29

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *