
Shahararren malami addinin Islama a Najeriya Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana dalilin da yasa ba sa sukar shugaban kasar Muhammadu Buhari a mumbarin wa’azi.
A cikin wani hoton bidiyon da aka ɗora a shafin Facebook an nuna malamin na jawabi, ku latsa wannan link don kallon bidiyon.
https://www.facebook.com/1407980569271285/posts/4503888376347140/
Wannan jawabi na malamin na zuwa ne a dai dai lokacin da ƴan ƙasar ke fama da tashe tashen hakula dake da nasaba da matsalar tsaro.
Inda ko a jiya saida shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Aika Da Babbar Tawagar Manyan Jami’an Tsaro Da Na Leken Asiri, Zuwa Jihohin Katsina Da Sokoto, Domin Daukan Mataki Akan ‘Yan Bindigan Da Suka Addabi Yankunan.
A ranar Jumma’a shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya aika da wata babbar tawaga ta manyan jami’an tsaro da na leken asiri karkashin jagorancin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd), zuwa jihohin Sokoto da Katsina, a matsayin martani ga karuwar ayyukan ‘yan bindiga a jihohin biyu don lalubo hanyoyin da za’a kawo karshen ‘yan bindigar.
Sauran ‘yan tawagar tsaron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, Darakta-Janar na DSS, Yusuf Magaji Bichi, Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da Shugaban Tsaro, Jami’in leken asiri, Manjo Janar Samuel Adebayo.
Shugaban kasar ya tura su jihohin ne domin dauko rahoton halin da ake ciki nan da nan da shawarwari game da hanyoyin da za a bi, don magance rashin tsaron da ya addabi yankunan.
Haka zalika shugaban kasar yayi alkawarin bazai daga kafa ba, a yunkurin tabbatar da tsaron rayuwar al’ummar Nijeriya, a duk inda suke a kasar, Duk abin da ake buƙata za a yi shi, har sai an sami cikakkiyar nasara, kamar yadda shugaban kasar ya bayyana a shafinshi na kafar sadarwa ta Facebook.
Masu karatu me zakuce game da wannan matakin da shugaban kasar zai dauka?
Views: 20
