Bidiyo: “Sarkin Musulmin Najeriya ya mayar da martani kan waƙar Davido”

Anyi Kira Ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Da Yasa Baki Akan Bidiyon Wasa Da Sallah Wanda Mawaki Davido Ya Fitar.

Al’ummar musulmi a Najeriya na cigaba da tafka muharawa a kafofin sada zumunta a kan wani faifan bidiyon da mawaki Davido ya fitar, inda a cikin bidiyon wakar aka hango wasu mutane sunyi shiga irin ta musulmi tare da kambarta sallah a wani waje mai kama da masallaci inda mutanen suna cikin sallar kawai suka koma tikar rawa yayin da mai rera wakar yake kan wani gini dake dauke da amsa kuwwar kiran sallah yana rero wakar daga can.

Tun bayan fitar bidiyon da bai yiwa al’ummar musulmi dadi ba, al’ummar musulmin kasar suna cigaba da suka tare da caccakar mawakin akan ya goge bidiyon ko kuma ya sake gyara bidiyon ya goge wurin da musulmin ke kallo a matsayin raini zuwa ga addinin Islama.

Yayin da wasu kuwa ke kira ga mai Alfarma Sarkin Musulmi da ya fito ya kalubalanci bidiyon a fili a madadin al’ummar musulmi kasar.

Meye ra’ayin ku kan wannan batu?

JaridarSokoto

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *