
Ana Raɗe-raɗin Buhari Zai Zarce a Karo Na Uku
Wani rahoto yayi ikirarin cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari na da niyyar zarcewa a karo na 3 akan mulki.
Rahoton ya ƙara da cewa, babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Abubakar Malami na son tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023 amma ya haƙura saboda aniyar shugaba Buharin ta son tsayawa takara a karo na 3.
Majiyar ta Sahara Reporters tace wasu majiyoyi a fadar shugaban ƙasa sun gaya mata cewa, masu ruwa da tsaki a fadar na yin dukkan mai yiyuwa dan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zarce a karo na 3.
Kazalika rahoton ya bayyana cewar, an gayawa masu son tsayawa takarar shugaban ƙasar a 2023 su janye aniyarsu. Inji majiyar ta Sahara Reporters.
Views: 15
