
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa zata sake bude shafin sada zumunta na Twitter a farkon wata mai kamawa, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin ministan yada labaru da al’adu na kasar Alhaji Lai Mohammed ta bayyana, a yammacin ranar talata sanarwa ta ce.
“Kwamitin shiga tsakani da aka kafa domin war ware takaddamar da ke faruwa tsakanin kamfanin sada zumunta na Twitter da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya, ya mika rahoton aikinsa zuwa ofishin ministan yada labarai da al’adu na kasa Alhaji Lai Mohammed, inda shi kuma zai mika shi zuwa ofishin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin yanke hukunci kan aikin da kwamitin ya gudanar a xikin makwanni biyun da suka gabata.
Idan ba’a manta ba gwamnatin kasar a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta rufe dandalin sada zumunta na Twitter, busa zarginsa da taimakawa yan tada kayar baya masu aikata ta’addanci a ciki da wajen kasar, zargin da kamfanin ya musanta, inda waau yan kasar ke ganin rufe Twitter a kasar yana da alaka da goge wani sako da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yake jan kunnen masu tada kayar baya a kasar.
Kunjinfa menen ra’ayoyinku?
Views: 18
