Idan aka kure mu zamu dakatar da Facebook, WhatsApp, Instagram—Lai Mohammed

Shafuka Sada Zumunta

Ministan watsa labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammad ya ce za su rufe daukacin sauran kafafen sadarwa a fadin kasar idan bukatar hakan ta taso, Mr, Lai Mohammad na magane ne a ranar talatar da ta gabata biyo bayan cigaba da sukar gwamnatin kasar da ake.

Jama’a da dama dai a cikin da wajen tarayyar Najeriya, na cigaba da korafe korafe dangane da dakatar da shafin sada zumuntar Twitter da gwamnatin kasar tayi.

Kimanin makonni biyu kenan dai da gwamnatin kasar ta dakatar da shafin sada zumuntar na Twitter biyo bayan zarginsa da taimakawa masu tada kayar baya a kasar, zargin da kamfanin na Twitter ya musanta.

Menene ra’ayoyinku a kai?

Views: 40

2 thoughts on “Idan aka kure mu zamu dakatar da Facebook, WhatsApp, Instagram—Lai Mohammed

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *