Duk wanda ya kara siyan kayan Isra’ila zai shafe shekaru 2 a gidan yari—Erdogan

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya haramta shigo da kayayyakin da ake kerawa daga Isra’ila, zuwa cikin kasar sa inda har yayi barazanar zartas da hukunci ga duk wanda ya sake shugo da kayan na Isra’ila kamar yadda wata majiya daga fadar mulkin kasar ta tseguntawa manema labarai.

Naji yar ta ce, “Mr Recep Tayyip Erdogan ya na duba yiwuwar sanya hannu a kan wani daftarin doka da zai tanaji hukuncin daurin shekara guda ko biyu, ko kuma cin tarar Dala dubu hamsin ga duk dan kasuwar da ya sake siyo kaya daga Isra’ila zuwa cikin kasar”

Sai da wasu na ganin hukuncin ya yi tsauri dayawa yayin da wasu ke bayyana gamsuwarsu da wannan hukunci, kunji fa ko menene ra’ayoyinku game da wannan batu, shin kuna ganin hukunci yayi dai dai?

Views: 104

One thought on “Duk wanda ya kara siyan kayan Isra’ila zai shafe shekaru 2 a gidan yari—Erdogan

Leave a Reply to Umar bello Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *