Hukumar NAFDAC Ta bayyana sakamakon gwajin da tayi akan Taliyar Indomie
Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa gwajin kimiyyar da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa taliyar Indomie lafiyarta kalau babu wani hadari a tare da ita.
A lokacin da take jawabi ga manema labarai, Adeyeye ta jaddada ingancin lafiyar Indomie da ake samarwa a cikin gida Nijeriya.
Ta tabbatar wa masu saye da sayar da kayayyakin abincin cewa, taliyar da aka janye ta “mai dandanon kaza ta musamman (Special Chicken Flabour)” a Taiwan da Malaysia ba ta tsallako cikin Nijeriya ba, don haka ba a sayar da ita ko’ina a kasuwannin Nijeriya.
A cewar shugabar ta NAFDAC, “An gwada jimillar samfura guda 114 na taliyar da abubuwan da suka hada da sinadarai daban-daban na ingancin abinci. Mun samu samfurori 58 daga masana’antu daban-daban, samfurori 24 daga kasuwannin Legas, samfurori 16 daga Abuja, da kuma samfurori 16 daga Kano.
An yi amfani da hanyoyi guda biyu don gwada samfurori daban-daban da aka tattara, su ne: dabarar nazari da ake amfani da ita don rarrabewa da gano abubuwan da ke tattare da sinadarai, da kuma dabarar nazarin da ake gano abubuwan sinadarai ta hanyar tantancewa.”
Da take bayani kan jinkirin da aka samu wajen fitar da sakamakon binciken, Adeyeye ta bayyana cewa, hakan ta faru ne saboda wasu kayan aiki da fasahar zamanin da aka yi amfani da su dole sai da aka shigo da su cikin kasar nan daga waje, sannan hukumar ta NAFDAC ta natsu ce ta yi aikin a kimiyance.
Views: 29
