Yadda wani Miji ya ɗirka wa ƙanwar Matar sa Ciki

Yadda wani Miji ya ɗirka wa ƙanwar Matar sa Ciki

Wata matashiya ta yadu a soshiyal midiya bayan mijin yayarta ya dirka mata ciki yayin da take zama tare da su.

Da take kare kanta, matashiyar ta bayyana cewa yayar tata ce ta nemi ta hadu da mijinta domin hana shi cin amanarta
Masu amfani da soshiyal sun bayyana ra’ayoyinsu game da bidiyon inda wasu da dama suka nuna rashin jin dadinsu
Wani labari ya yadu a soshiyal midiya game da wata yar Najeriya da ta bukaci kanwarta ta kwanta da mijinta domin hana shi neman matan banza a aje.

Matashiyar mai suna Onyiye ta yi ikirarin cewa yayar tata ta bukaci haka ne yayin da take dauke da juna biyu kuma bata iya kwanciya da mijinta.

Miji ya dirkawa kanwar matarsa ciki
“Sai Na Haife Dana”: Miji Ya Dirkawa Kanwar Matarsa Ciki, Dirama Ta Barke Hoto: @ojiugonwa/Twitter. Asali: TikTok

A cewar Onyinye, ta samu ciki da farko bayan ta kwanta da mijin yayarta sannan ta zubar da cikin.

Ta yi ikirarin cewa ta sake zubar da ciki sau biyu bayan wannan kafin ta yanke shawarar barin na ukun.

Sai dai kuma, yayar tata bata ji dadin lamarin ba inda ta koreta daga gidan, tana mai barazanar kwace shagon kwaliyyar da ta bude mata.

Onyinye, wanda ke tsoron rasa rayuwarta yayin zubar da ciki, ta nemi taimakon wasu mutaned kan su yi wa yayar tata da mijinta magana.

Sai dai kuma, da suka isa gidan yayar tata, sai suka tarar da barazana da tashin hankali daga wajen ma’auratan.

Jama’a sun yi martani.

Ku Latsa Wannan Jan Rubutun Domin Kallon BIDIYON

Labarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya, inda mutane da dama suka nuna kaduwa da jin haushin halin yar uwar da mijin nata.

Views: 31

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *