
Shahararren Malamin nan dake zaune a birnin kanon dabo mai suna Malam Muhammad Kofar Na’isa, ya karyata kansa da kansa a yau gaban jama’a wadanda suka taru domin halartar mukabalar da gwamnatin jihar Kano ta shirya a ranar yau, a karkashin kwamishinan kula da harakokin addinin Musulunci a jihar.
A zantawarsa da manema labarai Malam Muhammad ya bayyana cewa, “Ni fa ban auri wata Aljana ba idan ma ba aura to na yi mata saki ukku kuma duk abubuwan da nake yi kawai siddabaru ne, domin in samu na abinci kuma ina rokon gafarar mutane kowa da kowa” in ji shi kamar yadda ya bayyana a gaban manema labarai.
Idan baku manta ba Malam Muhammad Kofar Na’isa ya bayyana a kafar watsa labarai ta VOA inda ya ce yana yaro karami ya fada a hannun Aljana ta rene shi, kuma har ma ta ba shi diya ya aura yau dai an kawo karshe wannan tatsuniya ta malamin.
Views: 56
