Shugaban Ma’aikata na Gidan Janar Muhammadu Buhari, Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal Katsina, a madadin daukacin Ma’aikatan dake taimakawa Gwamna ta bangarori daban daban, yana taya Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari murnar zagayowar ranar haihuwar shi (29 ga watan Mayu, 1950), haka kuma a yau ne ya cika shekaru Shidda (6) a kan kujerar Gwamnan Jihar Katsina.
Wannan murna bata kauda alhinin da kullum muke ciki ba ta dalilin kalubalen tsaro, amma duba da fadi tashin da wannan bawan Allah yake yi wajen shawo kan wannan lamari da kuma ganin jihar Katsina bata kauce daga kan turbar ci gaba ba, muka ga ya dace mu karrama wannan Maigida namu ba tare da mun shaida mashi za muyi ba.
Muna rokon Allah cikin ikon Shi da buwayar Shi, Ya yaye mana wadannan ibtila’o’i da suka zamar mana tarnaki a wannan jiha da kasa baki daya. Allah Shi cigaba da yi wa Dallatu jagora, Ya kare shi tare damu daga dukkan sharri. Allah Shi kara budo wa jihar mu kofofin arziki da zaman lafiya.
Views: 42
