Ku kalli yadda sojoji suka yi artabu da yan bindiga

Yadda Sojojin Najeriya Ke Artabu

Jami’an rundunar sojin Najeriya sun fafata da yan ta’adda a jihar Borno inda suka samu nasarar kakkabe su a mabuyarsu da ke cikin wani dajin dake kan hanyar shiga babban birnin jihar wato Maiduguri.

Wani fai fan bidiyo ya nuna yadda jami’an rundunar sojin kasan Najeriya ke harbin bindiga a kwance domin karya lagon yan ta’addar da suka addabi yankin na Arewa maso Gabashin tarayyar Najeriyar.

Najeriya dai ta shafe shekara da shekaru tana fama da matsalar tsaro a sassan kasar daban daban musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar da kuma yankin Arewa maso Yamma da yankin kudancin kasar, inda a can ma ake fama da maso tada kayar baya.

Muna fatan Allah ya kawo mana karshen wadannan tashe tashen hankula ameen.

Views: 30

One thought on “Ku kalli yadda sojoji suka yi artabu da yan bindiga

Leave a Reply to Idris Maigari Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *