Mai taimakawa shugaban Najeriya, an harakokin da shuka shafi yada labarai da sadarwa, Malam Garba Shehu, ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin kasar da rufe kafar sadarwar Twitter a fadin kasar, inda ya ce, “Ba batun goge sakon da shugaba Buhari ya wallafa ne dalilin da ya sa aka rufe Twitter a kasar ba.
Kawai gwamnatin Najeriya ta lura da cewa shafin yana bada gudun mawa sosai wajen yada labaran karya da tunzura jama’a, domin bai goge irin sakonnin da yan ta’addar IPOB ke yadawa na furofaganda, ba amma kuma ya goge gargadin da shugaba Buhari yayi a kansu.
Wannan ne dalilin da yasa gwamnati ta dakatar da shafin, amma dakatarwar ta wucin gadi ce kuma za’a sake bude shafin ga yan Najeriya, nan ba da dadewa ba cikin wannan watan da muke ciki matukar kamfanin ya amince da sharuddan da gwamnati ta gindaya masa akan dakatar da sakonnin yan ta’adda.
Views: 22

Thanks