Labarin yadda Kishiya ta biyawa Kishiyarta kujerar Makka

Kishiya ta Biyawa Kishiyarta Kujerar Makka A Jihar Neja.

Ayayin da Hukumar Alhazan Jihar Neja ke cigaba da shirye shiryen fara aikin hajjin bana, Wani labarin da Limamin Tsalle Daya ya takulo lokacin da ya kai ziyara Ofishin hukumar dake Minna shine na wata mai niyya daga karamar hukumar Mashegu wacce ta biyawa kanta da kishiyar ta kujerar bana.

Wani Babban Jami’i a hukumar shine ya tseguntawa Limamin haka, da yake masa jawabi akan yadda shirye shiryen ke kan kankama.

Shin wani darasi yakamata mata su dauaka akan wannan kyautatawar da Baiwar Allar tayi ?

Views: 26

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *