Labarin yadda uba ya siyar da ɗansa a kan Naira dubu 400 a jihar Akwa Ibom

An Kama Uban Da Ya Sayar Da Dansa Kan Kudi 40k’ a Akwa Ibom

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta dauki matakin gaggawa tare da tabbatar da cafke wani uba mai suna Gabriel Ekpiri da ake zargi da siyar da dansa mai shekaru tara kan kudi naira 400,000 a karamar hukumar Itu ta jihar.

Wannan lamari mai cike da tada hankali ya jefa fargaba a cikin al’ummar yankin, lamarin da ya haifar da matukar damuwa game da walwala da tsaron yara.

A cewar jami’in hulda da jama’a na jihar, Odiko MacDon, rundunar ‘yan sanda tayi gaggawar zuwa inda ta cafke wanda ake zargin.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Gabriel Ekpiri ya amsa laifin da ya aikata kuma ya danganta abin da ya aikata a kan rashin kudi da ake fama da shi a Nijeriya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, Olatoye Durosinmi, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan aika-aika da Gabriel Ekpiri ya aikata.

Kwamishinan wanda ya bayyana hakan a matsayin dabbanci kuma sam ba za a amince da shi ba, Kwamishinan ya nuna matukar damuwarsa tare da yin kira da a gaggauta tabbatar da adalci kan wannan lamari.

Rundunar ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin don tabbatar da cewa an tattara dukkan bayanan da kuma bin doka da oda.

Daga Baba Waziri

Views: 39

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *