Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta dakatar da dukkan wasu ayyukan agaji a Nijar, kwana biyu bayan sojoji sun sanar da juyin mulki a ƙasar.
Ta ce a yanzu haka akwai mutum fiye da miliyan hudu da ke matuƙar bukatar agaji a Nijar din.
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniyar Antonio Guterres ya buƙaci sakin shugaban ƙasar Mohammed Bazoum wanda ke tsare a wajen sojojin ba tare da ɓata lokaci ba.
Shima ministan harkokin wajen Faransa ya ce shugaba Bazoum ɗin ya tattauna da shugaba Emmanuel Macron a safiyar yau kuma ya ce ana iya magana da shi sannan yana cikin koshin lafiya.
source: bbc hausa
Views: 37
