Gwamnatin tarayyar Najeriya bata maraba da gawar Fir’auna a ƙasar, ma’aikatar kula da adana kayayyakin tarihin ƙasar ta ce.
Babu wani yunƙuri da ake kawo yanzu na kawo ajiyar gawar Fir’auna a Najeriya kuma kona anayi to Najeriya bata maraba da wannan yunƙuri.
Fagen siyasa
SHUGABA BUHARI NE MINISTAN MAN FETUR
A mafi akasarin jihohin kudancin Nigeria har yanzu suna samun man fetur a farashin Gwamnati
Wannan wahalar mai da rashinsa duka a Arewa ya kare, dan Arewa ne Shugaban Kasa, kuma Shine ya nada kansa mukamin Ministan Man fetur, ina ne matsalar?
Ance wai lalacewar hanyoyi da karyewan gada a jihar Kogi inda tankokin mai suke bi su kawo mai Arewa ya haifar mana da wannan masifa, daga cikin masifar da muke gani shine hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi.
A dayan bangare kuma ance wai akwai man fetur din yana nan available a Arewa, masu sayar da man ne suka yin iskancinsu yadda suka ga dama, saboda rashin kyakkyawan Shugabanci a Kasar
Akwai wani rahoto kuma da na karanta jiya da daddare, ance wai hukumar DSS ta gargadi NNPC da masu sayar da mai akan cewa su saki mai wa jama’a, domin akwai mai din, imba haka ba DSS zata dauki mataki
Maigirma Shugaban Kasa kuma Babban Ministan man fetur na Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya yazo ya tarar da matsalar karancin man fetur da muke fama dashi duk karshen shekara, yayi kokari wajen kawar da matsalar.
Amma sai gashi anci amanarsa, mulkinsa na dab da karewa matsalar ta sake dawowa gidan jiya, fiye ma da yadda yazo ya tarar da ita, wannan abin bakin ciki ne da takaici
Yaa Allah Ka nuna mana karshen mulkin APC a 2023 lafiya
©Datti Assalafy
Views: 18
