Nine shugaban da yafi kowa adalci da jajircewa a Najeriya—Buhari

Albarkacin zagayowar ranar samun yancin kai a Najeriya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ua gudanar da jawabi a safiyar ranar juma’a inda ya ce.

Tun fara mulkin farar hula a shekarar 1999 Najeriya bata samun jajirtaccen shugaba iri na ba~Buhari

A cikin wani dan guntun rubutu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi albarkacin ranar samun ‘yancin kai a yau Juma’a, Buhari ya bayyana cewa babu gwamnatin da ta yaki ta’addanci kamar gwamnatinsa.

Buhari ya ce an samu nasarar sosai a yaki da ta’addanci a zuwan gwamnatinsa, kuma har yanzu tana kan wannan aiki.

Buhari ya kara da cewa a cikin shekara 6 gwamnatin sa ta yi aiyukka marasa adadi a cikin kasar nan, wadanda babu gwamnatin da ta taba yin irin su.

Views: 14

One thought on “Nine shugaban da yafi kowa adalci da jajircewa a Najeriya—Buhari

Leave a Reply to Bashir A Ahmad Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *