2023 Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya yi jawabi a kan shugabanci a wajen wani taron maulidin Annabi SAW a Abuja.
Ustaz Muhammad Awwal Olohungbebe ya wakikci tsohon Sarkin Kano, ya gabatar da jawabinsa a wurin taron.
Khalifa Sanusi ya yi bayani a kan shugabanci a doron Islama, yace ana bukatar wadanda za su kamanta adalci.
Ganin babban zaben 2023 ya gabato a Najeriya, Mai martaba Malam Sanusi Lamido Sanusi ya yi kira ga jama’a a kan abin da ya shafi zaben 2023.
A wani rahoto da muka samu daga Daily Trust, tsohon Sarkin na Kano ya yi kira ga ‘Yan Najeriya da su zabi shugabanni masu nagarta da hangen nesa.
Sarki Sanusi II ya fadawa al’umma cewa su hada da addu’a wajen zaben jagororinsu. Sanusi II bai kama sunan wani ko wata jam’iyya ba.
Dama dai tsohon sarkin na kano ya yi ƙaurin suna wajen tsoma bakinsa a harakokin
Views: 4
