Subhanallah: “An nemi Abduljabbar ya faɗi inda aka kira ANNABI SAW “Bunsuru da Bamaguje”

Abduljabbar Tare Da Malamai

An tambayi Abduljabbar ya faɗi inda aka kira Annabi “Bunsuru da Bamaguje da Arne” sai dai malamin da ya yi masa tambayar ya ce Abduljabbar ya kasa ba shi amsa.

Sannan Freedom Radio ta ruwaito cewa, Malam Abduljabbar ya gindaya sharuɗan tuba ga malaman da suka nemi ya tuba.

Sheikh Malam Abduljabbar Kabara ya sake gindaya sharuɗa ga malaman Kano, matuƙar da gaske suna so ya tuba daga abin da suke zargin sa da yi.

Malamin dai ya ce, har yanzu ba a gamsar da shi da hujjojin da suka fi nasa ba.

Kuma ya ce, “Ya za a yi na yi karatu awa biyu zuwa uku ina warware matsala, sannan a yanko minti biyar a ce sai na ce kaza cikin minti goma kacal.

A cewarsa “Me ya hana a ɗauko karatun gaba ɗaya a tattauna?”.

Sannan ya ƙara da cewa, indai za ayi haka, to ba a biyo hanyar da ake cewa, ana so na tuba ba, ba da gaske ake ba, ba kuma gyara ake cewa ana so ba.

Malamin kuma ya kuma ƙalubalancin malaman da su zo a biyo duk karatukan da yake yi, ba wai a gutsuro wata gaɓa ba.

Abduljabbar ya ce, duk kalaman da ake jingina masa cewa yayi ɓatanci ba gaskiya bane, hassalima shi ƙoƙarin kare musulunci ya ke.

Views: 34

One thought on “Subhanallah: “An nemi Abduljabbar ya faɗi inda aka kira ANNABI SAW “Bunsuru da Bamaguje”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *