Ku kwashi kayan ku, mu baza mu wahalar da wanda zai auri ya’yan mu ba~Sheikh Abubakar Usman Mabera

A ranar Assabar, wata tawagar jama’ar musulmi da suka fito daga Karamar hukumar mulki ta Wamakko, suka je neman auren wata mata a Hidikwatar kungiyar Izala Jos reshen jihar Sokoto, wajen shugaban majalisar Malamai na Jihar Sokoto, kuma babban limamin masallacin Mallam Buhari Dan Shehu dake nan cikin birnin Sokoto, wato Sheikh, Imam Abubakar Usman Mabera.
Abin ya faru shine: Lokacin da suka gabatar da abin da ke tafe dasu na nemawa ‘dan su mata, Imam Abubakar Usman Mabera ya basu kamar yadda shari’a ta tanada. Daga nan ne sai wadannan mutane suka fita waje, can sai suka sake dawowa cikin Office kowanensu dauke da Kwalayen minti, cingam, Biscuit, da Katon-Katon na lemu iri daban-daban da Goro, kamar dai yadda bakar al’adar da ake yi a jihar Sokoto tayin kayan SEE I LOVE, wadanda ake kusan kwashe dubu 300,000 ta tanada. Suna shigowa da su sai daya daga cikin su yace Allah ya gafartawa Mallam ga godiyar mu akan alherin da kukayi muna inji yaron da ya turo mu.
Views: 16
