
Na sanya na’urar daukar hoto wato Camera a turance dake a jikin waya ta domin in kama matata kuma nayi nasarar yin hakan, in ji wani magidanci.
Wani magidanci a birnin Zariya dake a jihar Kaduna ya bayyana yadda ya kama matarsa da kwarto dumu dumu.
Inda ya ce, an ɗauki tsawon lokaci ko kuma lokaci mai tsawo ana nusar da shi cewa matarsa na kawo kwarto a cikin gidan sa duk lokacin da ya yi wata tafiya.
Amma yake musantawa sai daga bisani ya sanya na’urar daukar hoto wato Camera a cikin gidan kuma ya fita waje.
Bayan ya dawo kwatsam sai idonsa ya gane masa wannan aika aika yayin da nan take ya ɗauki mataki a kanta.
Wato ya kora ta zuwa gidansu kamar yadda shafin Labarun yau da kullum ya ruwaito.
Views: 71
