Wa ke da alhakin gyara tarbiyya a cikin al’umma?

Wa ke da alhakin gyaran tarbiyya a cikin al’umma?

Daga__Abdulhadi Aminu.

Tunanin da ke cikin ƙwaƙwalwarmu shi ne in aka yi maganar tarbiyya to abu ne da ya shafi iyaye ko malamai, eh haka ne tabbas amma ba iya su ke da alhakin gyaran tarbiyya ba.

Sau tari muna wofintar da wannan ɓangaren duk da gayar muhimmancin da yake da shi, kowa abin da yake tunani shi ba ruwansa ai ba aikinshi ba ne!

Gyaran tarbiyya ba ne iya iyayenmu ba ne ko malamanmu, gyaran tarbiyya abu ne da ya hau kanmu baki ɗaya, idan kana ganin kai ba malami ba ne ko uba a yanzu ai baka san me zai je ya dawo gobe ba, koda baka zamo malamin makaranta ba ai za ka zamo uba, shin sai a lokacin za ka fara shiri?

A farko mu gyara kanmu a ɗaiɗaiku, mu kasance yadda muke son ƴaƴanmu su yi alfahari da mu, mu kyautata rayuwarmu ta yadda waninmu zai ji sha’awar zama da mu da yin mu’amala da mu saboda tarbiyya da kyan halayya da muke da.

Sannan duk inda muka ga mummunan abu to mu yi ƙoƙarin kawar da shi ta hanyar da ta dace, idan ma abin ya fi ƙarfinmu to mu sanar da ahalin abin, domin idan tarbiyya ta gyaru to mu ne da ƴayanmu za mu mori hakan, in ma akasin haka ne to mu ne za mu girbi abin da muka shuka.

Allah ya yi mana jagora.

Views: 119

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *